Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Khadib Zadeh ya na fadar haka a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa Iran ba zata taba zama taburi guda da washington ba matukar bata daukewa kasar takunkuman da ta dora mata ba.
Khatibzadeh Ya kammala da cewa taron da ake yi a birnin Vienna na kasar Austria dangane da yarjejeniyar JCPOA don share fage wa Amurka ta dawo cikin yarjejeniyar ne.
Amma ya zuwa yanzu Amurka bata yi wani abu a fili wanda yake nuna cewa tana son dawowa cikin yarjejeniyar ba.
342/